Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majilisar Wakilai kuma Dujiman Katsina Hon Aliyu Abdullahi Ahmed ya ce APC ta yi dacen shugaba.
A wata sanarwar da mataimaki na musamman kan yaɗa labarai Mr Francis Sardauna ya fitar ya bayyana sabon shugaban jam’iyar Farfesa Nentawe Yilwatda a matsayin wanda ya kware kan aikin gwamnati wanda hakan zai taimaka wa jam’iyar wajen samun tagomashi.
Ɗan majalisar da ke wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu ya bayyana zaɓen Farfesa Nentawe a matsayin shugaban jam’iyar APC ya tabbatar da halayen sa na sadauƙar da kai da iya shugabanci bisa adalci.
Ɗan majalisar na mai tabbacin cewa ƙarƙashin shugabancin Farfesa Yilwatda jam’iyar za ta ƙara samun tagomashi musamman yankunan karkara.
Dujiman ya sha alwashin bada goyon baya ga shugaban jam’iyar da kwamitin zartarwa na jam’iyar APC cikakken goyon baya domin cimma nasara musamman a zaɓuɓɓuka da ke tafe.
Ɗan majalisar ya kuma yi kira ga ya’yan jam’iyar na APC da su cigaba da aiki tuƙuru wajen gina jam’iyar da bada gudunmawar su wajen ciyar da ƙasa.
Kafin zaɓen sa a matsayin, shugaban jam’iyar APC ta ƙasa Furofesa Yilwatda na riƙe da muƙamin ministan jin ƙai.
