‘Lokacin daina yaƙi a Gaza ya yi’: Faransa na shirin ayyana Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Faransa ta sanar da shirin ayyana ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ƴanci a watan Satumba yayin babban zaman Majalisar Ɗinkin Duniya.

Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya sanar da hukuncin a daren ranar Alhamis wayewar Juma’a, inda ya ce hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a shiyyar Gabas ta Tsakiya, kamar yadda ya bayyana a wani saƙo ta kafar X.

Ya ce, babban abinda ke gabansu a yanzu shi ne kawo ƙarshen yaƙin Gaza tare da ceto al’ummar yankin.

Ya bayyana cewa, wajibi ne su gina ƙasar tare da tabbatar da dawo da martabarta da kuma bada gudumawarsu ga harkar tsaro ga kowane ɓangare a yankin gabas ta tsakiya.

A nasa ɓangaren, Fraministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana kalaman shugaban Faransan a matsayin abinda ka iya sake haddasa tashin-tashina tsakanin Isra’ila da Falasɗinu, yana mai cewa ba ƴanci ƴan Falasɗinu suke nema ba saida ƙoƙarin shafe Isra’ila da kafa ƙasarsu.

Yunƙurin Emmanuel Macron ya sa Faransa ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da suke fafutukar sake kafa Falasɗinu yayin da Norway, Ireland, da Sifaniya suka bi sahu.

By Babaji