Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar ADC mai hamayya a Nijeriya ta soki yadda gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke ci gaba da jan ƙafa wajen naɗa jakadun ƙasar a ƙasashen waje, tun bayan janye jakadun 109 a shekarar 2023.
Jam’iyyar ta gargaɗi ƙasar da cewa wannan matakin zai iya ɓata kimar Nijeriya a idon duniya. Sai dai tun tuni gwamnatin ta bayyana matsalar kuɗi a matsayin babban dalilin faruwar hakan.
Alhaji Ladan salihu, ɗaya ne daga jiga-jigan jam’iyyar ya shaida wa BBC cewa gwamnatin ƙasar ba ti yi wa ‘yan Nijeriya adalci ba har da waɗanda suke zaune a ƙasashen waje da harkoki da ayyukan diflomasiyya waɗanda suka dogara kacokan kan kasancewa waɗannan jakadun.
“Idan aka tuna, an samu masaloli kan batun biza a kwanakin nan a tsakanin Najeriya da Amurka wanda ya fi ƙamari a ɓangaren Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.”
Manhaja ta tuntuɓi ɓangaren gwamnatin Najeriya kan wannan batu, amma hakan ta ci tura.
Amma a wata hira da ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da gidan talabijin ta Arise ya ce gwamnatin shugaba Tinubu na fuskantar babban matsalar kuɗi da na tattalin arziƙi wadda ita ce silar kasa naɗa jakadun.
