Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta lashi takobin sake maka Shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a gaban kotun ɗaukaka ƙara bayan an hana ta shiga harabar majalisar a ranar Talata.
Cikin ɓacin rai, Natasha ta shaida wa ’yan jarida cewa za ta tattauna da lauyoyinta cikin gaggawa domin fara shigar da ƙarar, tana mai cewa matakin ya saɓa da hukuncin kotun da ta bayar da umarnin a mayar da ita kan kujerarta.
Lamarin dai ya biyo bayan yadda jami’an tsaron da ke gadin majalisar suka tare hanya suka hana tawagar motocinta shiga majalisar, duk kuwa da umarnin kotu na mayar da ita.
Ta kuma ce hatta dakatar da itan ma da farko ba ya kan ƙa’ida.
A cewar ta, “Yanzu zan je na tattauna da lauyoyina domin shirin ɗaukaka ƙara alabasshi kotu ta fassara mana abin da ya faru. Ni mace ce mai bin dokokin ƙasa.”
Sanatar ta kuma yi alla-wadai da matakin da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya ɗauka na hana ta shigar, inda ta ce hakan tamkar raina kotu ne.
Ta kuma ce, “Akpabio bai fi ƙarfin kundin tsarin mulkin Nijeriya ba. Ina so ’yan Najeriya su sani cewa ba Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ne ya mayar da ni Sanata ba.
“Duk da cewa ya tafi ɗaukaka ƙara, hakan ba yana nufin cewa ya soke hukuncin Mai Shari’a Binta Nyako ba ne kuma hakan ba zai dakatar da ni daga kasancewa Sanata ba.
“Mutanen Kogi ta Tsakiya ne suka zaɓe ni kuma su nake wakilta,” inji Natasha.
Tun da farko dai Sanatar ta yi yunkurin shiga majalisar tare da magoya bayanta amma, amma aka hanata, dole sai da ta sauka ta tafi a kafa.
An dai girke tarin jami’an tsaron da ba a saba ganin irin su ba a majalisar, inda aka ga wasu jami’an na duba motoci tare da ma takaita yawan waɗanda za su ajiya ababen hawa a wajen fakin na wajen majalisar.
Aƙalla an ga motocin sintiri na jami’an ’yan sanda guda biyar da aka girke a muhimman wuraren shiga majalisar.
