Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) da ke filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, sun ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Jami’an na hukumar shige da ficen sun ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne da safiyar ranar Alhamis.
Lamarin ya afku ne lokacin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta ke ƙoƙarin shiga jirgin British Airways zuwa birnin Landan.
Ganau a filin jirgin sun bayyana cewa Sanatar ta iso tashar jirgin na ƙasa da ƙasa ne tare da mijinta, Cif Emmanuel Uduaghan, amma sai jami’an shige da fice suka dakatar da ita tare da ayyana ta a matsayin “barazana ga tsaron ƙasa.”
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025, kafin a fara shiga jirgin da zai tashi zuwa Landan.
Fasinjoji sun ce, Sanata Natasha ta kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk tsawon lokacin da aka tsare ta, inda ta nace cewa jami’an ba su da hurumin riƙe fasfonta.
Ta riƙa gaya musu cewa kotu ba ta ba su hurumin riƙe mata fasfo ba. “Kotu ba ta ba ku wannan dama ba. Ba ku da ikon riƙe fasfona,” inji Sanata Natasha.
Babu wani ƙarin bayani na hukuma da aka bai wa Sanatar a lokacin da aka ƙwace fasfon, lamarin da ya ƙara hura wutar zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin.
An hangi mijinta, Cif Uduaghan, yana ta kiran waya cikin gaggawa yayin da tsaikon ke ci gaba da ɗaukar lokaci.
Bayan ’yan mintuna, an dawo mata da fasfonta ba tare da wani ƙarin bayani ba, lamarin da ya ba ta damar wucewa cikin gaggawa har ta samu shiga jirgin kafin a rufe ƙofa.
Lamarin ya tayar da ƙorafi da fargaba a tsakanin wasu daga cikin fasinjojin, inda masu kallo suka bayyana shi a matsayin abin kunya da kuma yiwuwar amfani da iko wajen wuce gona da iri.
Hukumar shige da fice ta ƙasa da kuma ofishin shugaban majalisar dattawa, har yanzu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan lamari ba.
