Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta umurci Sufeto-Janar na ‘Yan sanda da Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas da su biya diyyar Naira Miliyan 10 ga wasu gungun masu zanga-zangar #EndSARS bisa take haƙƙinsu.
Mai shari’a Musa Kakaki, wanda ya yanke hukuncin, ya gano cewa an ci zalin masu zanga-zangar EndSARS karo na huɗu da aka gudanar a ranar 20 ga Oktoba, 2024, domin nuna adawa da zalunci da harbe-harben da aka yi a ƙofar shiga Lekki a shekarar 2020.
A cikin hukuncin da ya yanke, alƙalin ya jaddada cewa, yayin da jami’an tsaro ke da aikin da kundin tsarin mulki ya tanada na tabbatar da zaman lafiyar jama’a, to dole ne a yi amfani da irin waɗannan iko bisa tsarin doka da dimokuraɗiyya.
“Matakin ‘yan sanda ga masu zanga-zangar ya saɓawa doka kuma ya keta haƙƙinsu na ‘yancin faɗin albarkacin baki, gudanar da taro, da kuma mutuncin ɗan Adam,” inji alƙali Kakaki.
Hassan Taiwo Soweto, Uadiale Kingsley, Ilesanmi Kehinde, Osopale Adeseye, Olamilekan Sanusi, da Osugba Blessing ne suka shigar da ƙarar a gaban kotun.
Har ila yau, akwai wasu ƙungiyoyin fafukar kare haƙƙi kamar: Yaƙin Kare Haƙƙoƙin Ilimi (ERC), Take It Back Moɓement (TIB), da Kamfen don Kare Haƙƙin ɗan Adam (CDHR).
Masu shigar da ƙarar sun ce su na gudanar da ayyukansu cikin lumana a lokacin da jami’an ‘yan sanda suka tarwatsa su da tsoratarwa da tsare su ba tare da wata ƙa’ida ba.
Masana harkokin shari’a da masu fafutuka sun yaba da hukuncin a matsayin wani muhimmin mataki na hana cin zalin daga hukumomin tsaro tare da tabbatar da ‘yancin ‘yan Nijeriya na gudanar da zanga-zangar lumana da taro.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ko kuma hukumar ‘yan sandan jihar Legas ba ta bayar da wani martani a hukumance kan hukuncin ba har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton.
