Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An bayyana cewa shugabanci na riƙo na ƙunigyar kasuwar Kantin Kwari Kano na tare da shugaban ƙungiyar ‘yan tebura wanda gwamnatin baya ta karɓe musu wurare ba ta mayar musu ba, kuma yanzu wannan gwamnati ta Alhaji Abba Kabir Yusuf mai sauraron ƙorafi da taimaka musu domin taimakawa al’umma wannan abu da suke yi abu ne na ljmana ba na tashin hankali ba kuma neman haƙƙi ta hanyar lumana da bin doka abu ne mai kyau, don haka shugabanci ƙungiyar kasuwar Kantin Kwari na riƙo na tare da wannan yunƙuri wanda munsan gwamna mai jin kukan wanda aka zalinta ne, kamar dai yadda ƙungiyar kasuwar Kantin Kwari Abdullahi Sharu Namalam ya bayyana a wajen gangamin taron da ‘yan ƙungiyar ‘yan tebura Multi Purpose and the Cooperatiɓe Society ƙarƙashin shugabancin Alhaji Aminu ɗan Falke ta gabatar a ranar Talata da ta gabata.
Haka kuma Sharu Abdullahi Namalam ya bayyana cewa wannan ƙungiya ta samu nasara wajen tsaftace kasuwar Kantin Kwari domin kawar da barazanar ambaliyar ruwa a wannan damuna wanda kuma hakan na daga cikin tsare-tsare na taftace kasuwar a zahiri da kuma baɗini daidai gwargwadon al’umma da wannan shugabanci na riƙo za su iya yi a wannan kasuwa ta Kantin Kwari da ke Kano. Kuma ya yaba wa ɗaukacin ‘yan kasuwar kan yadda suke bada haɗin kai wajen ganin komai ya tafi cikin tsari ta hanyar doka da sanin ya kamata.
Shi ma a jawabinsa shugaban ƙungiyar ‘yan tebura na kasuwar Kantin Kwari Alhaji Aminu ɗanfalke ya ce wannan yunƙuri ya samo asali ne sakamakon rasa wuraren sana’o’insu wanda abin ya shafi aƙalla mutane 3000 a wannan matsala ta ‘yan tebura domin tun farkon zuwa wannan gwamnatin suka miƙa sunayen mutum 1777 ga sakataren gwamnati na farko a wannan gwamnati sai kuma zuwan sabon shugaban kasuwar da gwamnati ta turo MD Alhaji Saad Dogon Nama sun miƙa ƙarin sunayen mutane 850 wanda ka ga sun kai kimamin da tsohuwar gwamnatin ta ƙwace mana wuraren mu a Kantin Kwari da muke neman gwamnatin Kano ta dubemu da idon rahama na adawo mana da wuraren in so samu ne ko kuma ayi mana abin da ya fi zama alkairi a duniyarmu da lahirar mu kamar dai yadda Alhaji Aminu Falke ya bayyana.
Taron dai ya samu halartar kwamishnan ciniki da masana’antu da zuba jari na Kano Alhaji Wada Sagagi wanda ya yi alwashin gwamnatin Abba za ta ɗauki matakin gaggawa domin dawo wa mai haƙƙi haƙƙinsa daidai yadda doka ta bada dama a wannan lokaci, inda shugaban kasuwar Alhaji Sa’ad Dogon Nama kan yadda aka yi wannan taro lafiya aka tashi lafiya.
