MEDCI ta yabi Gwamnatin Yobe kan gina hanyoyin karkara

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

Shugaban ƙungiyar Media and Disability Care Initiative (MEDCI), mai zaman kanta, Rajab Mohammed Isma’il, ya yaba wa ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Yobe bisa ayyukan gina hanyoyin raya karkara da birane a faɗin jihar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, a garin Potiskum, yayin da yake jagorantar tawagar ’yan jarida don ziyarar gani da ido dangane da ayyukan hanyoyin da gwamnatin jihar ta kammala da waɗanda ke gudana a jihar.

Ayyukan hanyoyin sun haɗa da hanyar Potiskum zuwa Ngojin mai nisan kilomita 2.5, hanyar Fadawa zuwa Daya mai nisan kilomita 5, a ƙarƙashin kulawar ma’aikatar ayyuka ta Jihar Yobe.

Rajab ya jaddada cewa waɗannan hanyoyin suna da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa yankunan karkara, inganta harkokin tattalin arziki, kiwon lafiya da kasuwancin al’ummomin da suke rayuwa a wannan yankin.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Maigarin Ngoji B, Malam Bulama Haruna, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Mai Mala Buni bisa wannan gagarumin aikin shimfiɗa hanyoyin mota. Ya ce aikin ya kawo sauƙi ga mazauna yankin da suka daɗe suna fama da matsalolin zirga-zirga, musamman a lokacin damina.

“A da, irin wannan ci gaba sai dai mu ji ana yi a wasu wurare. A lokacin damina, kusan ba zai yiwu a shiga ko fita daga Ngojin ba,” in ji shi.

Shima Malam Abdullahi Mohammed, a garin ya bayyana aikin gina hanyar a matsayin ɗaya daga cikin muhimman ayyukan ci gaba da suka taɓa faruwa a yankin cikin kusan karni daya.

Ya ce hanyar mai nisan kilomita 2.5 ta sauƙaƙa jigilar kayan amfanin gona da kuma kai marasa lafiya asibiti, inda ya jaddada cewa, noma shi ne babban aikin al’ummar yankin, kuma bisa ga wannan zai ci gaba.

Haka kuma, Malam Idi Muhammed Madaki, daga ƙauyen Daya, ya yaba wa Gwamna Buni bisa gina hanyar Fadawa zuwa Daya mai nisan kilomita 5.

Ya bayyana cewa al’ummar yankin sun dade suna jiran irin wannan ci gaba tun lokacin ƙirƙiro Jihar Yobe, kuma ganin aikin ya tabbata a wannan gwamnati babban ci gaba ne.

“Muna gode wa Gwamna Buni da duk waɗanda suka ba da gudunmawa wajen ganin wannan aiki ya kammala, musamman Kwamishina a ma’aikatar ayyuka ta Jihar Yobe.” in ji shi.

Shi ma Injiniya Saleh Mustapha, Injiniyan da ke kula da aikin titin Fadawa zuwa Daya, ya ce aikin yana tafiya daidai da yadda aka tsara, kuma za a kammala shi cikin wa’adin da aka ƙayyade tare da tabbatar da inganci.

By ukarofi