Super Falcons ta lashe Kofin WAFCON bayan doke Moroko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Super Falcons ta Nijeriya ta yi nasarar lashe Kofin Afirka na mata (WAFCON) karo na goma bayan doke takwararta ta Moroko da ci 3 da 2 a wasan ƙarshe.

Da fari, Atlas Lionesses ce da zura ƙwallaye biyu a ragar Super Falcons a zangon farko na wasan ta hannu ƴan wasa Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy.

Daga bisani a minti na 64 Esther Okoronkwo ta farke ɗaya a bugun fenareti bayan Nouhaila Benzina da taɓa ƙwallo da hannu a lokacin da Folamide ta bugu ƙwallo daga gefe raga.

Mintuna 19 da ƙarƙare wasan ne sai Ijamilusi ta farke ƙwallo ta biyu, inda a minti na 88 Jennifer Echegini ta zura ƙwallon da ta bai wa Nijeriya nasarar lashe kofin.

A buga wasan ne a filin Olympics dake birnin Rabat na ƙasar Moroko, lamarin da ya bai Super Falcons damar sake lashe kofin tun a shekarar 2018 da ta lashe.

By Babaji