
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Asabar Shugaba Bola Tinubu ya taya Super Falcons ta Nijeriya murnar lashe Kofin Ƙasashen Afirka (WAFCON) karo na 10.
Super Falcons sun yi nasarar ne bayan farfaɗowa da suka yi a yayin da aka tafi hutun rabin lokaci ana shan su ƙwallo biyu da nema, inda daga bisani suka yi nasara da ci 3 da 2 akan takwarorinsu na Moroko.
A saƙon da aka wallafa a shafinsa na X, Shugaba Tinubu ya bayyana farin cikinsa ga ƙungiyar, inda ya ce sun yi amfani da damar da suka samu wajen kare martabar Nijeriya.
“Sun sake yin nasara! Zakarun Afirka a karo na 10”, kamar yadda aka wallafa.
Haka ma matar Shugaban ƙasar, Sanata Oluremi Tinubu, ta jinin wa ƙungiyar bisa nasarar da suka samu a yayin jajircewarsu.
“Na taya ku murna, kyawawa kuma abin ƙaunarmu Super Falcons, bisa gagarumar nasararku ta lashe Kofin Ƙasashen Afirka na Mata karo na 10”, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.
Ta kuma miƙa godiyarta ga Allah wanda ya ba su nasarar a yayin da suka yi aiki tuƙuru wajen cimma hakan.
