Za a rasa ayyuka idan Dangote ya fara raba fetur kai-tsaye – NOGASA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Dillalan Man Fetur da Iskar Gas ta Nijeriya (NOGASA) ta nuna rashin amincewa da shirin da matatar Dangote ta yi a baya-bayan nan na samar da man fetur kai-tsaye ga masu amfani da shi, tare da kaucewa tsarin da aka saba da shi.

Shugaban NOGASA, Benneth Korie, ya bayyana damuwarsa cewa wannan matakin na iya kawo cikas ga masana’antar mai da iskar gas, tare da jefa dubunnan ayyuka al’umma cikin haɗari da kuma kawo cikas ga tsarin kasuwanci na masu samar da kayayyaki a duk faɗin ƙasar.

Idan za a iya tunawa, matatar man Dangote ta bayyana shirin fara samar da man fetur kai tsaye domin kawo ƙarshen kwarar masu amfani da shi daga ranar 15 ga watan Agustan 2025.

Matatar ta bayyana hakan ne a ranar 15 ga watan Yuni, 2025, inda ta bayyana cewa za ta tura sabbin tankokin 4,000 na man fetur da dizal kai-tsaye ga ‘yan kasuwa, dillalan man fetur, masana’antun, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu amfani da mai, da kuma kaucewa hanyoyin da aka saba bi.

Amma a cewar Korie, shawarar da Dangote ya yi na raba mai kai tsaye ga manyan ƙungiyoyi, kamar kamfanonin sadarwa da otel, ya nuna gagarumin sauyi a fannin.

Membobin NOGASA, waɗanda ke zama masu shiga tsakani matatun mai da masu saye, su na fargabar cewa wannan sabon tsarin rabo zai sa ayyukansu su daina aiki.

“Wannan sabon salo ne a masana’antar man fetur da iskar gas, inda yanzu Dangote ke samar da kayayyaki kai tsaye ga masu amfani da shi, musamman MTN, kamfanoni, otel-otel, da sauran su, ‘yan ƙungiyar NOGASA ne masu samar da man fetur, ta yin hakan, ayyuka da yawa su na cikin haɗari,” inji Korie.

Korie ya yi ƙarin haske kan illar da ke iya haifarwa, yana mai nuna cewa da yawa daga cikin mambobin NOGASA da ma’aikatansu na iya rasa ayyukansu.

Wannan a cewar ƙungiyar, zai yi tasiri ba kawai ga rayuwar mambobinsu ba, har ma da tattalin arzikin Nijeriya.

By ukarofi