Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wanda ya kafa kuma Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, a ranar Talata, ya ce, ‘yan kasuwar ƙasashen duniya su na cike da takaicin kafa sabbin matatun mai da kuma yadda ake gudanar da ayyukan man fetur a nahiyar Afirka.
Dangote ya bayyana cewa matatarsa ta na shigo da kimanin gangar ɗanyen mai miliyan 10 daga Amurka da sauran ƙasashe a kowane wata.
Dangote ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar da jawabin sa na musamman a taron ‘West African Refined Products Pricing and Markets Deɓelopment Conference’ wanda Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta shirya a Abuja.
A cewarsa, kamfanonin mai na ƙasashen waje (IOCs) su ne suka fi wahalar da shi a tafiyarsa wajen ginawa da kuma fara aikin matatar man.
Ya ce, bayan kammala aikin ginin matatar, babbar matsalar da suka fara fuskanta ita ce samun ɗanyen man da za a tace.
“Lokacin da muka fara aikin, abin da aka ɗauka a matsayin mai sauƙi shi ne samar da ɗanyen mai, musamman ganin cewa Nijeriya na samar da gangar mai miliyan 2 a rana. Amma sai muka gano cewa mun yi kuskure,” inji Aliko Dangote.
Attajirin ya ce, maimakon su riƙa sayen ɗanyen mai kai tsaye daga masu samar da shi a Nijeriya a farashi mai sauƙi, sai suka riƙa saya daga manyan ’yan kasuwa na duniya.
Ya bayyana cewa waɗannan ’yan kasuwan suna sayen ɗanyen mai daga Nujeriya su kuma sayar musu da shi a farashi mai tsada.
“Tabbas, kamar yadda muke magana a yau, muna sayen kusan gangar mai miliyan 9 zuwa 10 a duk wata daga Amurka da sauran ƙasashe,” Alhaji Aliko Dangote.
Dangote ya ƙara da cewa kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL) ya ba su ɗanyen mai daga lokacin da suka fara aiki har zuwa yanzu.
“Sun yi ƙoƙari sosai. Amma mun sha sosai da IOCs. IOCs su ne waɗanda suka fi wahalar da mu a duk tafiyarmu,” inji Dangote.
