Daga ABDULLAHI HASSAN YARIMA
Ya lura ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, duk lokacin da ya dawo gida matarsa da ‘ya’yansa na hira kawai sai ya ji an yi shiru kamar mutuwa ta ratsa, irin yadda muke cewa mu na yara yayin da ake cikin surutu kawai aka yi shiru batare da sanin dalilin yin shirun ba. Har sai da watarana ya kasa yin shiru ya yi magana a fusace. “Wato ga munafuki ya zo ko?”
Ba wai hira ce kawai ba a so ya ji ba, hirar ma ba a so a yi da shi. Ga shi dai matarsa ce wacce suka shafe fiye da shekara 30 tare. Kuma ba wani tashin hankali ko faɗa suke yawan yi ba. Kuma ‘ya’yansa ne da ya haifa tare da ita sai dai sannu a hankali kawai ya ga an mayar da shi saniyar ware. Yaran sun fi damuwa da mahaifiyarsu fiye da shi.
“Ka ga wannan ita ce matata.” Watarana yace da ni lokacin da zaro wayarsa daga aljihu ya nuna min. Don ko ya shiga cikin gida to shi kaɗai yake rayuwa a cikin ɗaki. Ban taɓa zaton wanda ya kai shekarun ritaya na game a waya ba sai da na haɗu da shi.
Ba shi ne mutum na farko da ya yi min irin wannan ƙorafin ba. Maza da yawa na shiga yanayin kaɗaici da damuwa idan aka shiga shekarun gangara tsakaninsu da iyalan su.
Idan mutum na da mace fiye da ɗaya, za ka iya hasashen cewa ko baƙin kishi suke taya mahaifiyarsu, to amma abin mamaki waɗanda duk na yi hira da su kan wannan matsalar ba wanda ke da mace fiye da ɗaya.
Wataƙila tunani na farko da zai zo maka shi ne mahaifin nasu bai kyautata musu ba a lokacin da suke ƙanana. Idan har haka kake zato, to tabbas zan yi disappointing ɗin ka. Don daga cikin waɗanda suka yi min wannan ƙorafin akwai wanda ni shaida ne kan irin tallafin da ya yiwa ‘ya’yansa a rayuwa. Duk wani sacrifices da uba zai yi a kan ‘ya’yansa wajen gina musu rayuwa ya yi. To amma me ya sa za su yi watsi da mahaifansu a lokacin da ya fi buƙatar su?
Akwai wani abu da zai ba ka mamaki. Duk cikin waɗanda suka yi min ƙorafi ba wanda na ga ya kalli laifin ‘ya’yansa kaitsaye. Duk laifin matan suke kalla. A cewarsu matan ne ke zuga ‘ya’yansu su yiwa iyayensu maza tawaye. To amma har yanzu ina kallon lamarin wani iri. Ta ya haka zai ke faruwa?
“Ka da ka kuskura ka tsufa da mace ɗaya, don da zarar kun kai wasu shekaru za ta ke azabtar da kai ta hanyoyi daban-daban…” Wanda ya taɓa ba ni wannan shawarar shekararsa 61. Don shi a cewarsa ba iya janye yaransa matarsa ta yi masa ba. Ta hure musu kunne sun zama maƙiyansa a halin yanzu.
“Da zarar yaran su girma, za ka gane cewa ita kaɗai ka haifawa ‘ya’yan…” Inji ɗan shekara 59.
Wanda na buɗe rubutun da labarinsa har ce min ya yi: ya na nadamar haifar yaran da ya yi. To amma na alaƙanta hakan da damuwar da yake ciki.
To, amma abin tambayar me ye hikimar uwa wajen raba yara da mahaifinsu? Idan wata matsala ce tsakaninki da mijinki me ya sa za ki shigo da ‘ya’yanki ciki? Ko laifin na yaran ne? Me ya sa ko da mahaifiyarka ta zuga ka kan bujurewa mahaifinka za ka yi mata biyayya? Ko kuma kawai wani abu ne ɓery natural yara sun fi son kyautata wa iyayensu mata fiye da maza? Kasa fahimtar hakan maza suka yi da har ya sa suke zargin cewa mata ne da gangan ke janye ‘ya’ya? Ko wani laifi mazan suka yi a ƙarshe suke karɓar sakamako? Ko kuma kawai haka ƙaddarar wasu ke zuwa babu wani ƙwaƙƙwaran dalili?
Malam Khalid Musa da Bala Anas Babinlata ya ku ka kalli wannan lamarin kuwa? Don na san amsar wata tambayar an fi sauƙin gano ta a cikin experience a maimakon karatun littafi.
Yarima marubuci ne, ya wallafa ne a shafinsa na Facebook
