
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Kamfanin Rukunin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaba mai karɓar shawara, wanda tsare-tsarensa ke farfaɗo da harkokin masana’antu masu zaman kansu, lamarin da a cewarsa ke da tasiri ga tattalin arziƙin Nijeriya.
Ɗangote ya faɗi haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin Ministar Masana’antu da Kasuwanci, Dakta Jumoke Oduwole a matatarsa da ke Ijebu-Lekki a Jihar Legas.
Da ya ke jinjina wa Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarinsa wajen magance matsalolin raba ɗanyen mai, Ɗangote ya yaba masa kan mayar da tsarin biyan kuɗin man da Naira kaɗai da ƙasa ta amince da shi, lamarin da ya taimaka wajen farfaɗo harkar tattali cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya kuma yi wa shugaban ƙasar godiya wajen tabbatar da inganta hanyoyoyin raba ɗanyen mai a ƙasar wanda ya taimaka wa rage wahalar mai a gidajen mai.
Ɗangote ya ce, shirye-shiryen da Tinubu ya samar a fannin da ma wasu fannonin harkokin tattalin ya taimaka wajen haɓaka harkar tattalin arziƙin Nijeriya ta yadda hatta masu zuba jari sun gamsu da tsarin shugaban ƙasar.



