An buƙaci gwamnatin Katsina ta gina magudanan ruwa a jihar

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar Dokokin Katsina ta nemi gwamnati ta gina hanyar ruwa a Mara-Zamfarawa, Ɗanmusa.

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga ɓangaren zartarwa da ta gina hanyar ruwa a yankin Mara-Zamfarawa da ke cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa, domin kare hanyar daga ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa da wanda ke haddasa lalacewar hanya da kawo cikas ga zirga-zirgar jama’a da ababen hawa.

Wannan kira ya biyo bayan ƙuduri da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ɗanmusa, Hon. Aminu Garba, ya gabatar, inda ya nemi majalisar ta buƙaci gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gaggawa na gina hanyar ruwa a yankin.

Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen daƙile barazanar ambaliya da zaizayar ƙasa, tare da sauƙaƙa hanyoyin sufuri ga al’ummar yankin.

Ƙudurin ya samu cikakken goyon bayan majalisar, inda kakakin majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya bayar da umarnin a tura ƙudurin zuwa ɓangaren zartarwa domin a duba kuma a ɗauki matakin da ya dace.

By ukarofi