Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Iyalan Janar Murtala Ramat Mohammed sun gudanar da bikin murnar tunawa da hawan marigayi tsohon shugaban ƙasar Nijeriyar mulki.
Mohammed ya hau kan karagar mulki ne a ranar 29 ga Yuli, 1975, wanda ke nuna jajircewarsa wajen kawo sauyi wanda ke ci gaba da yin tasiri a tsarin mulkin Nijeriya da kuma burin Afirka na cin gashin kai.
Domin tunawa da cika shekaru 50 na wannan lokaci mai cike da tarihi, iyalan sun ce gidauniyar Murtala Mohammed (MMF) tana ƙaddamar da wani shiri na ayyuka na tsawon shekara guda da aka tsara domin yin nazari a kan tarihin da ya bari da kuma tsara sabbin hanyoyin ci gaban ƙasa.
“Za a fara taron tunawa da jarumin a watan Agustan 2025 tare da fitar da jerin shirye-shiryen tattaunawa gama da tarihin Murtala Mohammed, babban taro na kowane wata wanda zai gudana har zuwa Janairun 2026.
“Tattaunawar za ta haɗa kan masu tsara manufofi, shugabannin nazari da abokan ci gaba don magance muhimman batutuwan ƙasa kamar yaƙi da cin hanci da rashawa, sake fasalin ilimi, haɗa kan matasa, samar da abinci, kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire na zamani. Waɗannan zaman za su nuna sauye-sauyen da Janar Murtala Muhammad ya jagoranta da kuma samar da mafita mai dacewa ga yanzu da kuma nan gaba,” inji wata sanarwa daga iyalan.
“A ƙarƙashin jagorancin gidauniyar Murtala Muhammed Foundation ƙarƙashin jagorancin Dr. Aisha Muhammed-Oyebode, wannan bikin na da nufin amfani da wannan lokacin ba wai kawai don tunawa da marigayi shugaban da tasirinsa har ma don farfaɗo da wayewar ƙasa da ya kawo.
“Za a kammala bikin ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2026, inda za a gudanar da taron ƙasa da ƙasa a Abuja, taron zai haɗa shugabannin duniya, masana, da masu neman kawo sauyi, domin duba tasirin da Murtala Muhammed ke da shi a tsarin mulki da ci gaba a yau.
Za ta binciki yadda hangen nesan sa ke ci gaba da yin tasirin a gyare-gyare a duk faɗin Afirka da zaburar da sabbin shugabanni.
Idan dai ba a manta ba, Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yaƙin basasar da akai a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman balle yankin Biafra daga Nijeriya.
A wannan lakacin janar Murtala ya jagoranci rundunar sojin da suka murƙushe sojojin Biafra tare da kawo ƙarshen yaƙi basasar baki ɗaya kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.
Yana matsayin birgediya ne sojojin da suka yi juyin mulki na uku a Nijeriya suka naɗa Murtala a matsayin shugaban ƙasa, inda a watan Janairun shekarar 1976 aka kara masa girma zuwa janar mai anini huɗu, wato ƙololuwa kenan.
Har ila yau, a wannan lokaci ne Janar Murtala ya ƙirƙiro da sabbin jihohi 7 ya kuma bayyana buƙatar mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Abuja da kuma alƙawarin miƙa mulki ga fararen hula a shekarar 1979.
