
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba John Mahama na ƙasar Ghana, ya tabbatar da cewa ƴan Nijeriya da ke zaune a Ghana za su cigaba da kasancewa cikin aminci, inda ce babu ƙofar nuna ƙiyayya ga ƴan waje a ƙasar.
A jawabinsa yayin ziyara ta musamman a Ghana da Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu ta kai masa, Shugaba Mahama ya jaddada ƙoƙarin gwamnatinsa na cigaba da bai wa ƴan Nijeriya da kasuwancinsu tsaro, yana mai cewa za su cigaba da kiyaye dokokin ECOWAS musamman waɗanda suka bada damar zirga-zirgar al’umma a shiyyar.
An gudanar da zaman ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke birnin Accra a yayin da ake zaman ɗar-ɗar bayan ganin wani bidiyon zanga-zangar #NigeriaMustGo da ya karaɗe shafukan sada zumunta.
A sanarwar da Kakakin ministar, Magnus Eze ya fitar, ya ce Shugaba Mahama ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da kada ya ruɗu da ganin bidiyon, lamarin da a cewarsa ana yaɗawa ne da nufin ruɗar da al’umma.
Ya kuma tabbatar wa tawagar Nijeriyar cewa gwamnatinsa tana aiki tuƙuru wajen ganin ta tabbatar da tsaro ga dukkan ƴan Nijeriya a Ghana da ba su a dama dama da su a harkokin ƙasar kamar yadda ya ke a dokance.
