Daga UNCLE LARABI
Duk macen da ta bi huɗubar wasu malamai masu son zuciya ko ‘yan ‘social media’ kuma ’yan miyar ta yi daɗi, za ta mutu cikin wahala! Sun ce jima’i ba dole ba ne ga mace sai lokacin da ta ga dama kuma ta yarda ko ma ta ke so sannnan mijinta zai biya buƙatarsa. Bayan Allah da kansa ya ce; Bismillahir Rahmanir Rahim. Annisa’u harsun lakum har zuwa ƙarshen surar. Ma’ana:- Matanku gonakinku ne ku je musu duk sanda ku ka ga dama kuma ta duk inda ku ka so, banda dubura. Kun ƙaryata wannan ayar, saboda son zuciya.
Sun ce girki ba dole ba ne mace ta yi wa mijinta, bayan mata mafi daraja a duniya sun yi wa mazajensu girki.
Babu wani malami duk ilminsa duk shahararsa da ya isa ya ƙaryata cewar; Nana Khadijah Bint Khuwailad ba ta yi wa Manzo sallallahu alaihi wassalam girki ba.
Babu wani malami da ya isa ya ƙaryata cewar Nanah Aisha Bint Abubakar ba ta yi wa Manzo sallallahu alaihi wassalam girki ba.
Babu wani malami da ya isa ya ƙaryata cewar, Nanah Hafsat Bint Umar ba ta yi wa Manzo sallallahu alaihi wassalam girki ba.
Sauran matan Manzon Allah sallallahu alaihi wassalam duk sun yi girki a gidansa. Ba ’yan aiki ne suke yi masa girki ba duk kuwa da daraja irin ta matan nasa.
Sannan wacce ta fi kowa gata a duniya, Nana Fatima Bint Muhammad, ’yar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ta yi wa mijinta Sayyadina Aliyu radiyallahu ta’ala anhu girki duk da irin gatanta. Har muƙamin shugabar matan aljanna aka ba ta.
Sauran matan sahabbai sun yi wa mazajensu girki, sun yi musu biyayya. Hatta a nan baya-baya iyayenmu, banda waɗanda iyayensu ba su haura shekaru 50 ba, waɗannan su ‘ya’yan sa’anninmu ne, su ne kuma matan da aka ba wa tarbiyya a baya yanzu suka kasa ba wa nasu yaran tarbiyya, su ne matan da aka ba su kulawa ta addini yanzu suke rushe nasu kulawar yaran da tarbiyyar yahudanci da wasu al’adu da ba su shafi addini ba.
To, su kansu iyayenmu mata sun yi wa iyayenmu maza girki da kwanciyar aure ba tare da son rai ba har ta kai suka tara bataliyar ‘ya’ya cikin kwanciyar hankali da jin daɗin auren.
Na tabbata kaso 100 na matan da yanzu suke yin Facebook, manyan ba yaran ba. Wato irin sa’anninmu ’yan shekaru 50 ko 40 da ɗoriya. To, kaso 20 ma ba su taso sun ga iyayensu mata na wulaƙanta iyayensu maza ba, ba su taso sun ga gidajensu da ’yan aiki ba, mahaifiyarsu ke yin duk wata hidimar gida cikin girmamawa da kyautatawa, babu ƙorafi.
Kuma sun taso sun ga iyayensu mata ke yin girki wasu ma har da wankewa iyayensu maza kayan dai nasu da a yanzu ganda ta sa ya zama abin ƙorafi.
Akwai abubuwa da yawa, saboda shi yahudanci ne wannan ba sa ma complain akai sbd shi yahudanci ne.
Ba su ce kai yara makaranta ko ɗauko su daga makaranta ba haƙƙin mace ba ne, saboda da safe suna fita da kayan barci a jikinsu da zundumemen hijabi, wanda wasu da yawa ana ganin surorin jikinsu. Kuma da yake za a koya mata mota ta hau titi tana tuƙi cike da gadara, wannan haƙƙin da ba nata ba, ba sa ma saka shi a lissafi, saboda shi yahudanci ne.
To, ko za ku iya faɗa min cewar a wacce aya ko sura ko hadisi ko ijtihadin malamai ya zo cewar, haƙƙin mace ne ta fita yin cefane ko a kan titi ko a super market?
Duk sa’anninmu mata ’yan shekara 50, babu wacce ta taso taga mahaifiyarta na wannan shashancin na zuwa wajen mai kayan miya yin cefane ko zuwa kanti siyayya bare har a tsallaka zuwasSuper market. Wannan ɗabi’ar Yahudawa ce, amma kun ara kun yafa. Ba ma ku maganar ai ba haƙƙin mace ne ta fita ta yi ba, saboda za a samu ɗan abin da za a yi zubin adashi ko na duk sati ko wata-wata.
Zuwa biyan kuɗin wuta da na makarantar yara, su ma na ga ai ba haƙƙin mace ba ne ko? To, amma me ya sa ba ku yi ƙorafi akan wannan ba? Amsar ita ce, kawai saboda za a yi cuwa-cuwa.
Akwai abubuwa da yawa, amma sai a rubutu na gaba zan bayyana su.
Shi namiji da yake walkiya aka yi daga sama ya faɗo, ba shi da wani haƙƙi a wajen matarsa. Ya gina gida ko ya kama haya, ya kun ce ma ya yi mata kayan ɗakin komai da komai har gara kawai sai dai ita a kawo masa ita. Kada ta yi masa girki, kada ta yi shara ko wanke-wanke bare wanke gida, kada ya yarda ya kusance ta sai ta ga dama.
Sannan ya yi mata lefe ya biya sadaki. Ya biya mata buƙatunta, idan tana son kuɗin zuwa unguwa ko ‘saloon’ ko shafe-shafe ko cinye-ciyen kayan ƙwalam. Shi ga ɗan iska ko? Ba abin da za ta yi masa. To, ya zauna kada ya yi auren mana.
Aure a wajensa ai ba shi da amfani idan har a irin wannan tunanin naku za a tafi.
Malam Abdullahi Jibril Dankantoma, wanda ake kira da Uncle Larabi, ya rubuto ne daga Kano a Nijeriya, kuma za a iya samun sa a lambar waya kan 08065418892
