Taɓarɓarewa: Matata ta hana ni la’antar Buhari bayan ya rasu – Fayose

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa, matarsa ce ta gargaɗe shi da kada ya la’anci tsohon Shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari, lokacin da ya rasu a farkon watan Yuli.

“A Nijeriya mutane su na yaba wa mutum kawai bayan ya mutu,” inji shi a cikin shirin Siyasa na gidan talbijin na Channels a Juma’a.

“Lokacin da Shugaba Buhari ya mutu, na so na fito na zage shi, amma matata ta kira ni ta hana ni aikata hakan.”

Fayose, wanda ya daɗe yana sukar gwamnatin Buhari, ya bayyana cewa, marigayi tsohon shugaban ƙasar bai yi aiki yadda ya kamata ba a tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki.

“Za ku iya cewa, Buhari ya yi aiki? Ba na cikin masu yabon matattu, kada ku girmama ni idan na mutu, idan na mutu na tafi kenan.

“Lokacin da Shugaba Buhari ya ke gwamnati, dukkanmu mun san me ƙasar nan ta ke ciki, don haka kar da wani ya zo ya faɗa min cewa Shugaba Bola Tinubu bai yi aiki ba.”

Tsohon gwamnan na Ekiti ya ce, ba kamar Buhari ba, Tinubu yana aiki.

“Shi Tinubu ya na aiki, shin tsohon shugaban ƙasar ya yi aiki?

Da yake kare Tinubu, Fayose ya ce, “Nijeriya ƙasa ce marar lafiya, bai zai yiwu ta samu lafiya cikin sauƙi ba.

“Wane irin almara ne wani zai iya yi a cikin shekaru biyu? Halin da Nijeriya ta ke ciki ya tsananta. Tinubu ya gaji mummunan tattalin arziki.”

By ukarofi