
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Neja ta gargaɗi al’ummar da ke zama a wurare masu barazanar samuwar ambaliya akansu da su ƙaurace zuwa yankuna masu tudu.
Wani rahoto ya bayyana yadda wani ruwan sama da aka yi a safiyar ranar Lahadi ya shafe gonaki a Ƙananan Hukumomin Lapai da Paikoro a jihar.
A Lapai, aƙalla ƙauyuka 18 lamarin ya shafa inda ya lalata gonaki da dama yayin da ya jefa wasu masu yawa cikin haɗari.
Haka ma a Paikoro, gonaki a Kafin Koro sun lalace sakamakon ruwan safe da aka yi a Lahadin.
Don haka ne Gwamnatin jihar a wata sanarwa ta mai taimaka wa gwamna akan harkar yaɗa labarai, Jonathan Vatsa, ta kirayi al’ummar ƙauyukan da lamarin ya shafa da su gaggauta barin yankunansu domin ƙauce wa faɗawa cikin iftila’i.
Daga cikin ƙauyukan da ke fuskantar barazanar aukuwar ambaliya akwai; Dere, Eshi, Apataku, Tsakanabi, Kuchi Kakanda, Arah, Achiba, Rebba, Ebwa, Pele, Edda, Rigido, Gbami, Yawa, Baka, da kuma Muye.
A baya ne gwamnatin tarayya ta gargaɗi wasu ƙananan hukumomin jihar huɗu da su ƙaurace zuwa wasu yankuna masu tsaro yayin da ake sa ran samun ambaliya daga ranakun 31 ga Yuli zuwa 4 ga watan Agusta.
