Daga ABUBAKAR A. BOLARI Gombe
Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu, babban ɗan gidan sarauta daga zuriyar Bubayero, a matsayin Tafarkin Gombe ɗaya daga cikin sarautun da ake darajawa sosai a al’adun masarautar Hausa.
Wannan naɗin ya zo ne a matsayin yabo da girmamawa kan gudummawar da Dakta Daudu ya bayar ga masarautar da ƙasa baki ɗaya.
Dakta Daudu, wanda shi ne tsohon babban sakatare na tarayya, ya kasancce kwamishinan lafiya na farko a Jihar Gombe, daga baya ya riƙe muƙamin shugaban ma’aikata na Jihar Gombe sannan kafin daga baya a naɗa shi babban sakatare a fadar shugaban ƙasa.
Yanzu haka, shi ne kwamishinan tarayya a hukumar kula da ayyukan ma’aikata, yana wakiltar jihohin Adamawa, Gombe da Taraba.
Gogaggen jami’in gwamnati shi ne Ɗan Masanin Funakaye, kuma kakansa ne ya fara zama hakimin Gombe tun bayan da masarautar ta taso daga Gombe Abba zuwa Nafada, har zuwa kafa birnin Gombe na yanzu.
Sarautar Tafarki tana da muhimmanci a tarihi, inda a al’adance ake bai wa ɗan sarki ko babban ɗan uwansa wannan matsayi.
Tafarki yana da alhakin ba da shawara ga sarki, tsawatarwa idan ya zama dole, da kuma jagoranci na addini da na al’ada
Haka kuma, mai riƙe da wannan sarauta yana da cikakken damar shiga fada ba tare da wani shinge ba.
Asalin wannan sarauta ya samo ne tun zamanin Hausa Bakwai, inda aka ce Tafarki na farko ya fito ne daga Katsina a zamanin Sarkin Katsina, Umaru Dallaje, wanda ya naɗa ɗan uwansa Musa a wannan matsayi bayan sun sake haɗuwa a kusa da iyakar Borno da Nijar.
A yayin naɗin, Sarkin Gombe ya bayyana Dakta Daudu a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati mai daraja, wanda zurfin asalin gidan sa da ƙwarewarsa ya dace da rawar da zai taka a matsayin babban mashawarci ga masarautar Gombe.
Dakta Daudu, a hirarsa da wakilinmu, ya nuna farin ciki da godiya ga Sarkin da Majalisar Masarauta, tare da yin alƙawarin yin hidima cikin gaskiya da amana.
Ya kuma yi alƙawarin inganta zaman lafiya, haɗin kai da kare gadon tarihi na Masarautar Gombe.
