Pantami ya kirayi Tinubu ya karrama yarinyar da ta yi ta ɗaya a gasar Turanci kamar ƴan wasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya karrama Nafisa Abdullah Aminu, wadda ta zama gwarzuwa a gasar Turanci ta duniya da aka yi a Landon, irin yadda ya yi wa ƴan wasan Super Falcons da D’Tigress a lokacin da suka yi nasara.

Nafisa, mai shekaru 17 ɗaliba ce a makarantar Nigerian Tulip International College (NTIC) da ke Jihar Yobe, inda ta yi nasarar doke sama da ɗalibai guda 20,000 daga ƙasashe 69 ciki har da masu amfani da Turanci.

Lamarin da ya sa ake jinjina mata duba da yadda ta sanya al’ummar Nijeriya farin ciki da alfahari a idon duniya.

A wani rubutu a shafinsa na sada zumunta, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana nasararta a matsayin abinda ya samu sakamakon fahimta, horo, sadaukarwa da kuma taimakon iyaye da malamanta.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta karrama ɗalibar da irin kyautukan da ta bai wa ƴan wasa mata na Super Falcons da D’Tigress bisa nasarorin da suka yi a ƴan kwanakin nan.

Shehin malamin addinin ya shawarci da a bai wa Nafisa Dala 100,000, gida mai ɗakin kwana guda 3 da kuma babbar kyautar ƙasa ta OON, yayin da shi ma malaminta na Turanci a ba shi irin kyautukan da aka bai masu horarwa na ƴan wasa da jami’an gudanarwa.

By Babaji