Sarkin Daura ya tabbatar da sarautar Sarkin Gabas ga shugaban NLC reshen Jihar Katsina

Spread the love



Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‎Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, ya tabbatar wa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen Jihar Katsina, Kwamared Hussaini Hamisu Yanduma, da sarautar Sarkin Gabas na Daura.

‎Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar ɗauke da sa hannun Danejin Daura, Alhaji Abdulmuminu Salihu, a madadin Majalisar Masarautar.

‎Kwamared Hussaini Hamisu Yanduma, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta ƙasa, ya sami wannan sarauta ne saboda irin gudummuwar da yake bayarwa wajen ci gaban Masarautar Daura, da Jihar Katsina da kuma Nijeriya baki ɗaya a cewar masarautar.

Masarautar ta bayyana Alhaji Hussaini Hamisu a matsayin mutum mai biyayya ga masarautar Daura ga shi da taimakawa al’umma musamman ta fannin kiwon lafiya.

“Kasancewar ka shugaba a ƙungiyoyin ƙwadago daban daban shaida ce ta cancantar karrama wa da wannan sarauta,”inji Danejin Daura.

‎Haka kuma, Sarkin Ban Daura hakimin Yanduna ya tabbatarwa Kwamared Hamisu Hussaini Yanduma da sarautar gargajiya ta Sardaunan Yanduna.

‎ A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sarkin Ban Daura, wanda kuma shi ne Hakimin Yanduna, Alhaji Mohammad Shazaalli, ya ce wannan karramawa ce saboda kyautatawa da ke tsakanin shugaban ƙungiyar ƙwadagon da al’ummar Yanduna.

By ukarofi