Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnati ta ɗauki matakin rufe asibitocin ne bisa zargin gudanar da ayyukan jinya ba tare da cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa na buɗe cibiyoyin lafiya, da karya dokokin kula da lafiyar jama’a.
Kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya sanar da ɗaukan wannan mataki a lokacin da ya fara ziyarar gani da ido a asibitoci masu zaman kansu a jihar.
Cibiyoyin lafiyar da aka rufe sun haɗa da, G-11 Medicine Store , Dental Emergency da Ɗan Ƙofa Medicine Store, bayan da aka gano suna gudanar da ayyukan jinya ba tare da cika ƙa’idojin rajista ba, kana suna kwantar da marasa lafiya ba bisa doka ba.
Kwamishinan ya umarci waɗannan cibiyoyi da su koma ga hukumar lafiya ta jihar domin kammala duk wasu sharuɗɗan da suka wajaba kafin a ba su damar ci gaba da aiki.
Ya bayyana cewa ziyarar tantancewar za ta ci gaba a sauran sassan jihar
Hon Adamu Funtua ya jaddada ƙudurin gwamnati na tabbatar da dukkan cibiyoyin lafiya suna bin ƙa’idojin da doka ta shimfida don kare lafiyar al’umma
Kwanan baya sai da gwamnatin jihar ta rufe wasu kwalejojin kiwon lafiya tare da ba wasu wa’adin samar da kayan karatu a kwalejojin da ke jihar.
