Wa ya rage bai mutu ba a Gaza?

Spread the love

Haƙiƙa babbar tambaya ce a idanu cewa wa ya rage bai mutu ba a Zirin Gaza? Amma gaskiyar lamarin in ka ga mutum na rayuwa yanzu a Gaza to kawai jiran ko-ta-kwana ya ke yi za ta kwana ko dai za a kwana da shi a lahira. Duk bayanin da wani mai sharhi zai yi sai dai ya zama kwatance kasancewar shiga Gaza ga mai daukar rahotanni ba abu ba ne mai sauƙi. Hatta masu raba kayan agaji ma kan fuskanci kisa balle a je ga wani mai ɗaukar labaru musamman na kafar labarum da Isra’ila ke ɗauka na jin tausayin Falasɗinawa ko mara baya ga samun ‘yancin Falasɗinawan. Ko an kawar da kai kan Gaza irin hotunan da a ke gani na yadda yunwa ke kassara yara da tura da yawan su kabari ya zama dole a sassauta ƙin jinin su da wasu ke yi ba ma irin ƙasashen yamma da wasun su ke ɗaukar Falasɗinawa da zama fitannun mutane da su ka ƙi amincewa da zama ƙarƙashin mulkin Isra’ila. A tarihi an san lokacin da a ka kafa ƙasar Isra’ila a 1948 cikin ƙasar Falasɗinawa inda a hankali Yahudawa su ka riƙa taruwa da haƙiƙancewa wajen dawo da hatta harshen su da wasu ma ba su iya ba. Inda a ka ware mu su bai wadatar da su ba sai su ka ci gaba da mamaye Karin filaye na Falasɗinawa da dirar mikiya kan duk wanda ya nemi ƙalubalantar hakan.

A fili ya ke ƙungiyar neman ‘yancin Falasɗinawa ta PLO ta ke takatsantsan ga yanayin gwagwarmaya inda ta riƙa yin ɗabi’u na diflomasiyya kamar yanda gogan ƙungiyar marigayi Yasar Arafat ya yi amma hakan bai hana a ka ƙulla ma sa maƙarƙashiya ba. Kun ga yanzu shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas da ke birnin Ramallah kamar baya nan don yanda a ka kaskantar da jagororin Falasɗinawa da zama masu magana da fatar baki ko ma dai fushi a can cikin zuciya. A yau ba wani Bafalasɗine da ya aminta daga farmakin Isra’ila. Kowaye sojojin Isra’ila za su iya kai wa hari. Tsananin azabtar da Falasɗinawa da Isra’ila ke yi ya sa wasu mazauna Gaza neman bijirewa ƙungiyar mayaƙan Hamas da buƙatar a kori ‘yan ƙungiyar ko a samu sararawa ta rayuwar bauta ƙarƙashin Isra’ila. Wasu su kan shirya zanga-zanga ta neman korar Hamas daga Gaza da zummar samun sauƙi.

Alamu na nuna ba lallai don mayaƙan Hamas ne kaɗai Isra’ila ke kunna wuta a Gaza ba wannan don kawo ƙarshen duk wani yunƙuri ne na batun ‘yancin Falasɗinawa. Menene laifin waɗanda su ka taru don karɓar kayan agaji da sojojin Isra’ila kan buɗewa wuta ta kashe na kashewa ta raunata na raunatawa. Duk kiran da ƙungiyoyin agaji ke yi na a bar abinci da magani su shiga Gaza hakan na samun turjiya daga Isra’ila. ƙasar ta Yahudawa ke ba da izini ga shigar koma mene ne zuwa Gaza. Kamar yanda na taɓa bayyanawa a baya nadamar Isra’ila kawai in ta ƙarƙashe Falasɗinawa da gangan shi ne wai za ta yi bincike daga nan magana ta kare sai ka ji shiru Malam ya ci shirwa.

Daya daga ‘yan majalisar zartarwa na ɓangaren tsaro na Isra’ila Zeeɓ Elkin ya ce su na shirin kara keɓe wasu sassa na Gaza da hakan koma baya zai kawo ga faɗin ƙasar Falasɗinawa ko da ma a karshe a iya kafata daga matsayin ta na jeka-na-yi-ka. Elkin ya ce abu mai ciwo shi ne waɗanda ya zaiyana da abokan gaba wato Falasɗinawa ko Hamas za su cigaba da rasa filaye. Elkin ya yi barazanar matuƙar Hamas ta ci gaba da abun da ya ce jan kafa kan yarjejeniyar tsagaita wuta to za ta rasa filayen ta da har abada ba za ta sake samun su ba. Shin yanzu ma ba a kan ƙasar Falasɗinawa ƙasar Isra’ila ta ke zaune ba? Duniya za ta bar Isra’ila ta cinye ƙasar Falasɗinawa ta kuma bautar da su ba tare da iya taɓuka komai ba tun da an samu babbar ƙasar duniya na mara ma ta baya? Wannan na nuna adalcin duniya bai gama cika ba matuƙar dokokin ƙasa da ƙasa ba sa tasiri kan wata ƙasa ko kan ƙasashe masu makaman ƙare dangi.

Taron ƙarfafa batun kafa ƙasar Falasdinu gefe da Isra’ila ya gudana daidai lokacin da yunwa ta ta’azzara a yankin Gaza don yakin da a ke gudanarwa da ya doshi shekaru 2.

Saudiyya da Faransa ne ke ƙashin bayan taron a birnin New York na Amurka wanda a ke tsammanin zai yi tasiri.

Abun da zai dau hankali shi ne sauya manufar da Faransa ta yi inda yanzu ta ke mara baya ga kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin maslahar kawo ƙarshen fitinar Falasɗinawa da Isra’ila.

Saudiyya na kan gaba a ƙasashen Larabawa da ke kanbama kafa ƙasar Falasɗinu da babban birnin ta zai zama a gabashin birnin ƙudus.

Za a gudanar da irin taron don bin kadun manufar a watan Satumba a babban zauren Majalisar ɗinkin Duniya inda shugaban Faransa Emmanuel Macron da hadin gwiwar Yarima Muhammad bin Salman na Saudiyya za su jagoranta.

Daga fara wannan yaƙi a ranar 7 ga Oktobar 2023, an kashe fiye da Falasɗinawa 56,000 akasari mata da ƙananan yara.

Burtaniya ta ƙi amincewa da caccaka daga Isra’ila kan wa’adin da ta bayar na cewa za ta mara baya ga kafa ƙasar Falasɗinu.

Tun daga baiyana aniyar Burtaniya ta marawa yunƙurin kafa ƙasar Falasɗinawa baya ta ke samun suka daga masu goyon bayan Isra’ila cewa hakan tamkar kyautatawa ƙungiyar Hamas ne.

Matsayar ta Birtaniya ta biyo bayan amincewa da Faransa ta yi kan hanyar warware taƙaddamar Falasɗinawa da Isra’ila ita ce kafa ƙasar Falasɗinu.

Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya dau matakin ne bayan duba yanda yunwa ke gallabar Falasɗinawa musamman ƙananan yara da ke yankwanewa don tsananin yunwa.

A nan Burtaniya ta ba da wa’adi zuwa Satumba na lallai Isra’ila ta duba kadun yunwa a Gaza ko kuma Burtaniya ta goyi bayan kafa aasar Falasɗinu.

Shugaba Trump da ke goyon bayan Isra’ila shi ma ya ce matakin na Burtaniya ai kamar sakawa Hamas ne da Isra’ika ke cewa kuma kamar kawar da ido ne kan kutsawa da Hamas ta yi cikin Isra’ila a 2023 ta yi kashe-kashe.

Burtaniya ta ce ba daidai ba ne a ɗauki matsayin na ta cewa la’ada ne ga Hamas da ta ke ɗauka ƙungiyar ta’addanci, amma ta yi hakan ne don al’ummar Falasɗinawa da ke cikin uƙuba.

In za mu tuna Afurka ta kudu ta taba yunƙuri a baya hart a kai kara kotun duniya don a dakatar da Isra’ila daga kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa da sunan murƙushe mayaƙan Hamas.

Tsawatar da kotun duniya ta yi bai yi tasiri kan Isra’ila ba da ma ta shashantar da hurumin kotun cewa kamar shirme kawai ma ta ke yi.

Gomman mutane Falasɗinawa da ke fama da yunwa sun rasa ran su yayin da a ka buɗe mu su wuta a mashigar Zikim ta karɓar kayan tallafi zuwa mazuna arewacin Gaza. Zikim ne yankin da mazauna arewacin Zirin kan tsallaka don isa inda a kan tara kayan tallafi.

Kimanin mutum 48 su ka mutu kamar yanda alƙaluman asibitin Al-Shifa su ka bayyana inda da dama su ka samu raunuka.

Wasu alƙaluman ma sun nuna waɗanda a ka kashen sun fi yawan waɗanda a ka ambata.

An ga gawawwaki a waste yayin da masu sauran shan ruwa ke ɗauke da tallafin fulawa don tsananin ƙarancin abinci da ke addabar Zirin.

Ba a tantance zuwa rubuta labarin nan wanda ya buɗe wutar ba kuma ba a samu martanin Isra’ila ko sojojin Isra’ila da kan buɗe wuta kan masu karɓar agajin ba.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jakadan Amurka Steɓe Witkoff ke shiga Isra’ila don tattaunawa da zummar kawo ƙarshen yaƙin da ya kai wata 22.

Witkoff na jagorantar tattaunawa a madadin Amurka don yiwuwar dakatar da yaƙin da sako sauran kamammun Isra’ila da ke Gaza.

Har yanzu a na mamakin rashin nasarar jagorancin Amurka ga batun dakatar da buɗe wuta a tarukan da a ke ta yi a Doha ko Alkahira na Masar.

ƙasar ƙatar da Masar na da ƙarfi a tsakanin ƙasashen Larabawa amma su ɗin ma ba za su iya wuce makadi da rawa ba sai sun jira su ga inda Amurka ta fuskanta. Siyasar duniya ta fito fili tun yaƙin da ƙasashen Larabawa su ka yi da Isra’ila a 1967 da kowa ya koma kare fadar sa.

KAMMALAWA

Abun da zai iya yiwuwa a yanzu shi ne buɗa ‘yar ƙofa da abinci zai iya kai wa wasu sassan Gaza ko a ce a nuna kamar an ɗan samu sauƙi yara na samun kulawa a Zirin. Kafa ƙasar Falasɗinawa zai zo ko ba yanzu ba da goyon baya ko ba goyon bayan manyan ƙasashen duniya. Wanda Allah ya ba wa nisan kwana zai iya shaida wannan lokacin kuma zai iya faruwa ko ba a zamnin rayuwar mu ba. Zalunci ba zai ɗore ba har abada. Mutuwa ba bakuwa ba ce kuma ko a gado mutum zai iya mutuwa in lokacin ya yi bisa ma ga zahirin misalign yadda tsohon Firaministan Isra’ila mai matuƙar ƙin jinin Falasɗinawa Ariel Sharon ya mutu bayan shekaru ya na magashiyyan.

By ukarofi