‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka ga manema labarai kan nasarorin da rundunar ta ta samu a watan da ya gabata.
Ya bayyana cewa a cikin su, mutane 14 aka kama da laifin fashi da makami,sai mutane 22 da zargin aikata kisan kai.
Haka kuma yan sandan sun Kama mutane 25 da ake zargi da aikata fyaɗe,mutane 20 kuma da zargin lalata kayan gwamnati.
Akwai mutane 26 da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi, sauran mutane 194 da aka kama da aikata laifuka daban-daban da ba a bayyana ba, kamar yadda DSP Sadiq ya faɗa.
Ya kuma sanar da cewa yan sandan sun gano dabbobi guda 199 waɗanda a cikin su 161 shanu ne da aka sace.
“Akwai guda 68 da motar hawa guda uku da aka gano”inji DSP Sadiq.
Sauran kayan da ‘yan sandan suka gano a wajen waɗanda ake zargi akwai baburan hawa guda biyu da miyagun ƙwayoyi da ba a riga an gane adadin su ba tare da ganyen da ake zargi tabar wiwi ce.
Kwamishinan ‘yan sanda a Jihar Katsina CP Bello Shehu ya bayyana irin taimako da gwamnatin jihar ke bai wa ‘yan sanda da kuma gudanarwa da al’ummar ke badawa da yace sun taimaka wajen inganta tsaro a jihar.
Sai yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da bada gudunmawa da goyon baya ga rundunar ‘yan sandan domin samun nasarar daƙile miyagun ayyuka a jihar.
