
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗaruruwan mata waɗanda galibinsu tsofaffi da masu shayarwa ne suka kewaye tituna a Gusau, babban birnin jihar Zamfara domin nuna kaɗuwarsu game da munanan hare-haren ƴan bindiga da suka yi ƙamari a ƴan kwanakin nan a sassan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun taho ne daga Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda inda suka nufi gidan gwamnatin a Gusau tare da neman a gaggauta dakatar da kashe-kashe da garkuwa da mutane da suka yawaita a yankin.
An gudanar da zanga-zangar ne bayan wani irinsa da aka yi a birnin makonni biyu da suka gabata sakamakon rasa rayukan sama da mutane 100 a ƙauyukan Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Lilo, Bangi da wasunsu.
“Mun gaji. Mazajenmu suna tsare, ƴaƴanmu suna fama da yunwa. Ba za mu koma gida ba sai an ba mu tabbacin samun kariya”, inji wata Maimuna Adamu.
Wani mai suna Auwalu Umar ya koka a fili inda ya bayyana yadda ya rasa baki ɗaya ƴan gidansu a sanadiyyar harin ƴan bindiga. “Sun kashe mahaifina, mahaifiyata, ƴan uwana maza da mata. Ni kaɗai na ke rayuwa ba tare da taimako ko kyakkyawan fata ba.”
Mazuana da dama sun tabbatar da harin ƴan bindiga a jihar Zamfara ƴan kwanakin nan sun yi ƙamari musamman a garuruwa kamar su Sabon Garin Damri, Dakko Butsa, Tungar Abdu Dogo, Tungar Sarkin Daji, Sadeda, da Tungar Labi, waɗanda baki ɗaya suke cikin haɗari.
