Da Ɗumi-Ɗumi: Daga ƙarshe, Mawaƙi Kwam 1 ya bada haƙuri kan lamarin filin jirgin sama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Daɗaɗɗen mawaƙin nan mai suna Wasiu Ayinde Marshal da aka fi sani da Kwam 1 ya bada haƙuri sakamakon al’amarin da ya faru a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja a ranar Talata.

A wata sanarwa, Kwam 1 ya bayyana da-na-saninsa game da lamarin, saidai ya musanta batun cewa ya zo ɗauke da giya a wani kofin zuba ruwan zafi, inda a cewarsa ruwa ne ya ke ɗauke da shi a ciki.

Ya ce, yana fama rashin lafiyar da ke sanya shi shan ruwa akai-akai, wanda likitoci suak shawarce shi a kai.

Ya kuma ce, sai da jami’ai suka tantance kofin babu komai a cikinsa kafin ya samu damar shiga cikin filin.

Da ya ke bada haƙurin, Kwam 1 ya bayyana cewa lallai bai yi nufin taka kowace doka ko ƙoƙarin haifar da tsaiko a filin ba.

Akan haka ne ya miƙa saƙon bada haƙuri ga Fadar Shugaban Ƙasa, Ma’aikatar Sufurin Jiragen sama, FAAN, NCAA, ValueJet da al’ummar Nijeriya a gida da waje.

By Babaji