Al’ummar yankin Funtua sun buƙaci gwamnatin Katsina ta inganta tsaro

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An yi kira da gwamnatin Jihar Katsina da ta fito da wasu dabaru da sabbin tsare-tsare na inganta tsaro a yankin.

Wannan kira na ɗaya daga cikin matsaya da mazaɓar Nassarawa a ƙaramar Funtua a gaɓar wajen taron sauraren buƙace buƙace na al’umma da za a sanya a kasafin kuɗi na 2025.

Wasu daga cikin buƙatar al’ummar mazaɓar suke buƙatar sun haɗa da samar da aikin yi ga matasa da tallafawa mata masu ƙananan sana’o’i.

Shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua kwamred Mannir Suleiman ɗan asalin mazaɓar ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da ya ƙirƙiro da wannan dandali da ya ce zai ƙara ba gwamnati dama na sanin ainihin matsalolin al’ummar jihar musamman mazauna karkara.

Sai yayi kira ga gwamna Dikko Raɗɗa da ya bi sau da ƙafa wajen aiwatar da buƙatar da aka gabatar domin cigaban al’umma da jihar baki ɗaya.

Kwamred Suleiman ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa bisa abubuwan alheri da ya gudanar a yankin Funtua da yace shakka za su taimakawa yankin wajen tattalin arziki da inganta ilimi da kiyon lafiya.

Ya bada misali da manyan tagwayen hanyoyi da sabuwar jami’ar koyon aikin lafiya na gwamnatin tarayya da sauran wasu ayyuka na raya ƙasa a yankin.

Ya tabbatar da cewa ƙungiyar su a shirye ta ke ta bada nata gudunmawa ta hanyar bada shawarwari ga gwamnati ta yadda za a ciyar da jihar gaba.

Kwamred Suleiman ya sanar da cewa ƙungiyar su ta samar da ofishin ƙungiyar wanda nan bada jimawa ba za ayi bikin ƙaddamar wa bayan an kammala gyare-gyare.

By ukarofi