WAEC ta lashe amanta: Kaso 62.96 sun ci jarrabawar 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Cibiyar Gudanar da Jarrabawar Makaratun Yammacin Afirka (WAEC) ta fitar da sakamakon jarrabawa na daidai ga ɗaliban da suka rubuta na 2025 a yau Juma’a.

Hakan ya biyo bayan kuren da aka samu a yayin fitar da sakamakon a karon fari.

Shugaban WAEC a Nijeriya, Dakta Amos Dangut ya bayyana damawa kan yadda aka samu tsaiko a karon fari wajen fitar da sakamakon, wanda ya nuna an samu gagarumar faɗuwa.

Ya ce, hakan ya faru ne musamman kan jarrabawar Turanci ɓangaren canka-canka, wanda ya haifar da sakamakon na kuskure.

Bayan gyaran ne aka gano cewa aƙalla kaso 62.96 na ɗalibai 1,969,313 da suka rubuta jarrabawar sun yi nasara a darussa biyar ko sama da haka ciki har da darussan Turanci da Lissafi.

Haka ya nuna an samu cigaba akan kaso 38.32 da aka fitar da fari.

Ga waɗanda ke da ƙorafi har zuwa yanzu kan sakamakon, hukumar ta bada adireshi kamar haka domin isarwa: https://waecinternational.org/complaints.

By Babaji