Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shahararren shugaban ‘yan ta’adda a jihar Zamfara, Bello Turji, ya saki mutum 32 da ya sace, tare da amincewa da daina kai hari kan manoma, bayan jerin ganawa da wasu malamai a maɓoyarsa.
Fitaccen malamin addini, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, ne ya bayyana hakan yayin wani taron addini a Kaduna a ranar Litinin.
Malamin ya ce Bello Turji ya ajiye wasu daga cikin makaman sa ne bayan ganawa da shi a ƙaramar Hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Ya ce al’ummar Shinkafi ne suka roƙi malamai su shiga tsakani don roƙon Turji ya ba su damar zuwa gonakinsu da ke cikin daji. Ya ce an yi ganawar ne sau uku a watan Yuli, a dajin Fakai.
A cewarsa: “Mun gana da Turji, ɗan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila. Jita-jitar cewa ɗan Bakkolo ya mutu ba gaskiya ba ce. Waɗannan ne ke addabar yankin, kuma dukkansu sun amince da shawarwarin zaman lafiya, ciki har da miƙa wasu daga cikin makamansu a matsayin alamar goyon bayan zaman lafiya.
“Sun miƙa makamai a matakai daban-daban kuma sun ba wa jama’ar Shinkafi damar zuwa gonakinsu da ke cikin daji a bayan kogin da ke kaiwa maɓoyar Turji. Mun kuma amince cewa Fulani za su iya zuwa gari ba tare da an tsangwama ko kashe su ba daga masu sa kai.
“Shi (Turji) ya kuma saki mutum 32 da ya yi garkuwa da su a matsayin wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya,” inji Malam Yusuf, inda ya nuna bidiyon wasu daga cikin fursunonin da aka sako da irin mawuyacin halin da suka fuskanta wajen isa maboyar Turji.
Ya bayyana cewa mutanen da aka sako, ciki har da yara da mata, sun kwashe kusan wata huɗu a hannun ‘yan ta’addan. Wasu daga cikin matan sun haihu a daji yayin da daya daga cikinsu ta kamu da cizon maciji.
Malam Yusuf ya ce tun bayan yarjejeniyar, yankin Shinkafi ya fara samun zaman lafiya, inda mutane ke ci gaba da noma ba tare da fargabar sace su ba.
Ya ce malamai na ci gaba da kokarin shawo kan Turji domin ya amince da cikakken zaman lafiya, amma ba su buƙaci ya miƙa duka makaman sa ba, domin kada hakan ya sa wasu ƙungiyoyin makiyaya su kai masa hari.
Ya gargaɗi wasu malamai da ke sukar Turji a kafafen sada zumunta cewa hakan ba zai haifar da da mai ido ba illa ƙara dagula lamura.
Ya ce kodayake yarjejeniyar da Turji ba za ta kawo ƙarshen matsalar tsaro gaba ɗaya a Zamfara ba, amma al’ummomin yankin da ke ƙarƙashinsa na jin daɗin zaman lafiya.
Malamin ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu, Mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da Sanata Shehu Buba bisa goyon bayan hanyar sulhu maimakon amfani da karfi wajen magance matsalolin tsaro.
A watan Oktoba, Turji ya yi gargaɗi cewa zaman lafiya ba zai samu a jihar Zamfara ba har sai dakarun gwamnati da ƙungiyoyin sa kai sun daina kai wa Fulani hari.
A cewarsa a cikin wani bidiyo: “Shi ya sa muke kira gare ku da ku zo mu hada kai domin zaman lafiya ya samu a Zamfara, a daina zubar da jini. Bindiga da hare-haren sama ba za su hana mu ba, domin ba ma jin tsoron mutuwa.
“Rikicin siyasa tsakanin Gwamna Dauda Lawal da Bello Matawalle, wanda yanzu shi ne ƙaramin Ministan Tsaro, ya janyo matsalar tsaro ta ta’azzara. Dukansu ba su damu da rayuwar al’umma ba,” inji Turji.
