Ba za mu karɓi fursunoni kamar wasu ƙasashe ba – Gwamnatin Tarayya ga Amurka

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ƙi amince wa ƙulla yarjejeniya da Amurka na karɓar waɗanda aka koro a ƙarƙashin tsarin Shugaba Donald Trump na korar waɗanda ba ƴan Amurka ba zuwa wasu ƙasashe, inda ta ce Nijeriya ba za ta bi sahun Rwanda, Eswatini ko Sudan ta Kudu ba.

Da ya ke ganawa da manema labarai, Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ya tabbatar da cewa matsayar Abuja tana nan yadda ta ke, domin a cewarsa hakan zai haifar da barazana ga harkokin tsaro da tattali.

A watan Yuli Ministan ma’aikatar, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa Washington na yunƙurin matsa wa ƙasashen Afirka karɓar ƴan ƙasar Venezuela, waɗanda daga ciki akwai fursunoni da ƙasarsu ta ki amince wa karɓar su.

Ya ce, karɓar irin waɗanda ga Nijeriya abu ne mai wahala domin akwai matsaloli da dama a ƙasar, wanda a yanzu ma adadin al’ummarta ya kai kimanin miliyan 230.

A ƙarƙashin tsarin, wanda Kotun Ƙoli ta yi hukunci a kai, akwai batun barin waɗanda aka koro su je wasu ƙasashen da ba nasu ba yayin da aka ƙi karɓar su a asalin ƙasashensu.

Lamarin da ya sa wasu ƙasashen Afirka suka amince da hukuncin, inda tuni suka fara karɓar ƴan Vietnam, Jamaica da Yemen.

Kamar Rwanda, ta amince ta karɓi sama mutane 250 da aka koro bisa wasu sharuɗɗa.

By Babaji