Tinubu ya yi jimamin rasuwar Audu Ogbeh, ya jinjina wa hidimarsa ga Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kaɗuwarsa game da rashin tsohon Ministan Noma kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh, wanda ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin ƴan ƙasa masu kishi da suka sadaukar da kansu ga cigaban Nijeriya.

A safiyar yau Asabar ne iyalan Ogbeh suka sanar da rasuwarsa a wata sanarwa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga a wata takarda ya ce Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin tsayayye akan kalamansa musamman kan al’amuran da suka shafi hidimta wa al’umma.

A tun shekarun 1970s marigayin ya shiga harkar siyasa baya ga kasancewar sa manomi kuma babban jami’in harkokin gudanarwa wanda burinsa shine samar da ci-gaba a kowane fanni a Nijeriya.

Ya kuma ce, za a yi kewar kyawawan manufofi da ƙwarewarsa ga ci-gaban ƙasa.

Shugaban ƙasar ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Benuwai da iyala da ƴan uwa da abokan arziƙi bisa babban rashin, yana mai musu fatan samun haƙurin juriyan rashinsa.

By Babaji