
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matatar mai ta Ɗangote a wani karo, ta sake rage farashin litar fetur daga N850 zuwa N820 a faɗin Nijeriya.
Anthony Chiejina, jami’in yaɗa labaranta, ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya ce, an samu ragin N30 ga kowace lita, wanda a cewarsa, hakan zai fara aiki ne daga ranar.
Ƙari akan haka, kakakin ya ce nan ba da jimawa ba matatar a ƙoƙarinta na samar da mafita ga harkokin makamashi, za ta fara fitar da tirelolin gas na CNG a faɗin Nijeriya, wato daga ranar 15 ga watan Agusta, 2025.
