
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya tabbatar da cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta haɗa hannu da Hukumar Kula da Fina-finai ta Ƙasa NFC, a ƙoƙarinsa na faɗaɗa harkar tattalin ƙirƙira a jihar.
Ya kuma yaba wa hukumar bisa ƙoƙarinta na inganta harkokin gudanar da fina-finai da tasirinsu a gida Nijeriya da ƙasashen waje.
Inuwa Yahaya ya bayyana haka ne a yayin da Darakta Manaja na hukumar, Dakta Ali Nuhu ya kai masa ziyara a Gidan Gwamnatin jihar da ke garin Gombe, ranar Talata.
A wata takarda da Daraktan yaɗa labaran NFC, Brian Etuk ya fitar, gwmnan ya bayyana aniyarsa ta mayar da jihar fage na baza ayyukan da suka shafi ƙirƙira, lamarin da a cewarsa ka iya bunƙasa harkar tattali a jihar, shiyyar Arewa ta Gabas da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ce, hakan zai yiwu ne ta hanyar haɗa hannu da cibiyoyi da hukumomin da lamarin ya shafa, wanda zai taimaka wajen bada horo, inganta matasa da samar da ayyuka a jihar.
Ya ƙara da cewa, a tsawon shekaru shida na mulkinsa, gwamnatinsa ta duƙufa wajen samar da ci-gaba tare da bada gudunmuwa ga harkokin da suka shafi ƙirƙira duba da yadda suke da gagarumin tasiri ga harkar tattali.
A nasa jawabin, Dakta Ali Nuhu ya yaba wa gwamnan kan ƙoƙarinsa na samar da shirye-shiryen da suka shafi ci-gaba acikin al’umma da harkokin ƙirƙira waɗanda su ma suke taimaka wa bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa.

