Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan wani gari da ƴan bindiga su ka kai a unguwar Manatau a ƙaramar hukumar Malumfashi inda suka kashe mutane 13.
Sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya fitar,ya bayyana cewa yan bindigan sun kashe waɗannan mutane a wani masallaci lokacin da al’ummar Musulmin unguwar ke gudanar da sallar Asuba.
Kan haka mutanen unguwar Manatau suka ɗauki fansa inda suma suka kashe da dama tare da ceto wasu mutanen da ‘yan bindiga suka sato daga ƙauyen ruwan sanyi a cewar kwamishinan.
Dr Ɗanmusa ya bayyana cewa al’ummar unguwar sun sami Babura guda uku da bindaga ƙirar AK 47 guda biyu daga hannun ƴan bindagan.
Akan haka ne yace, gwamnatin Katsina ta ƙara kai sojojin sama da na ƙasa da kuma jami’an ƴan sanda domin dawo da zaman lafiya a unguwar.
Kwamishinan ya jinjina wa al’ummar yankin bisa namijin ƙoƙari da suka nuna wajen fatattakar ƴan bindigan.
Ya yi ta’aziya ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu a lokacin hare haren ƴan bindiga a unguwar tare da jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na kakkaɓe sauran ƴan ta’adda a faɗin jihar.
