NCAA ta hana fasinjoji barin salula a kunne yayin tashi da saukar jiragen sama

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Ƙasa NCAA, ta umarci fasinjoji da su riƙa kashe wayoyin hannunsu a yayin tashi da saukar jiragen sama.

Daraktan yaɗa labarai da bai wa fasinjoji kariya na hukumar, Michael Achimugu ya bayyana hakan a wani rubutu ta kafar X.

Ya ce, an mayar da tsarin gudanar da salula da sauran kayayyakin lantarki bai-ɗaya a Nijeriya, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin.

Hukuncin ya biyo bayan taron gaggawa da masu ruwa da tsaki a ranar Talata.

A yayin haka an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi rashin riƙe girma daga wasu fasinjoji, masu gadi na filayen jiragen sama da dai sauransu.

By Babaji