Kwamishinan lafiyar Jihar Katsina ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban asibitin Zango

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

A cigaba da ziyarar manyan asibitoci da gwamnatin jihar ke ginawa, kwamishinan lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya kai ziyarar dubiya a asibitin Zango da ke ƙaramar hukumar zango.

A yayin ziyarar, kwamishinan ya zagaya sassa daban-daban na asibitin da ake aiwatar da gyare-gyare, inda ya yaba da aikin dake gudana ya daceda ƙa’idar kwangila da ingancin kayan da aka tsara.

Kwamishinan ya tattauna da kamfanin da ke jagorantar aikin, tare da jan hankalinsu kan muhimmancin kammala aikin akan lokaci.

Hon Musa Adamu Funtua ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sanya inganta harkar lafiya abu mai muhimmanci. Saboda haka, gyaran wannan asibiti na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na inganta cibiyoyin lafiya a dukkanin ƙananan hukumomi 34, domin jama’a su riƙa samun ingantacciyar kulawar lafiya kusa da su.

Ya kuma jaddada cewa za a ci gaba da gudanar da irin wannan kulawa a duk inda ake gudanar da ayyukan lafiya, domin tabbatar da amfanin jama’a da kuma ingancin ayyukan gwamnati.

By ukarofi