Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Muƙaddashin gwamnan Jihar Katsina Malam Farouk Lawal Joɓe bayan hare haren ƴan bindiga yayi ƙamari a kudancin jihar.
Yakamata shugaban ƙasa cikin gaggawa ya umurci manyan shugabanin Sojojin ƙasar da su murƙushe ƴan ta’adda a jihar tun kafin su murƙushe jihar Joɓe ya ce.
Wannan kira ya biyo bayan wani muhimmin hari da yan bindigan suka kai a wani masallaci a unguwar Mantau inda suka kashi mutane 13.
“Cikin biyayya muna roƙon shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya umurci jami’an tsaro da su kawo ƙarshen hare haren ta’addanci a jihar,”inji muƙaddashin gwamnan.
Ya bayyana cewa al’ummar jihar na buƙatarsa samun zaman lafiya da kwanciyar hankali domin su tafiyar da harkokin yau da kullum.
Joɓe ya ƙara da cewa ,manoma, ƴan kasuwa da sauran al’ummar jihar bai kamata a ce koda yaushe suna zama cikin fargaba ba.
Ya yaba wa jami’an tsaro da ke tabbatar da tsaro a jihar bisa jajircewa da na mijin ƙoƙari da suke wajan yaƙan ta’addanci a jihar.
Muƙaddashin gwamnan wanda shine mataimakin gwamnan jihar ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatin jihar da haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya da jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarin su wajen kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.
