
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a riƙe asusu guda huɗu na wasu bankuna da aka alaƙanta su da tsohon shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, Mele Kolo Kyari bisa zargin badaƙala, makirci, wulaƙanta aiki da sauya akalar wasu kuɗaɗe.
Mai Shari’a Emeka Nwite ya yi hukuncin a ranar Talata, ƙarƙashin ƙarar da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFCC ta shigar ta Lauya Ogechi Ujam.
Dayake EFCC ta nemi a riƙe asusun na watanni biyu domin ta samu damar kammala bincike akansu, mai shari’ar ya bada kwana 30 kaɗai da zaɓin a sabunta riƙon su matuƙar masu binciken suka buƙaci ƙarin lokaci.
Daga nan ne alƙalin ya ɗage sauraren ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Satumba, 2025 domin EFCC ta sake bada ba’asi a kai.
Asusun da lamarin ya shafa suna haɗa da: 0017922724 – ɗauke da sunan Mele Kyari; 0018575055 – da sunan Guwori Community Development; da kuma 0018575141 – da sunan Guwori Community Development Foundation Flood Relief.
Masu bincike sun yi zargin cewa Kyari tare da wasu mambobin iyalansa ke gudanar da asusun bankunan, sannan ana amfani da su wajen hada-hadar wasu kuɗaɗe a ake zargin suna da alaƙa da na NNPCL da wasu kamfanonin mai.
Aƙalla ₦661,464,601.50 ne ake zargin an yi wasu haramtattun ayyuka da su ta asusun bankunan da aka zayyano.
