Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sakataren Gwamnatin Jiha (SGS), Barista Abdullahi Garba Faskari ne ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnatin jiha, inda ya nuna damuwar gwamnati kan lamarin da ya faru tare da nanata aniyar gwamnati wajen cigaba da wanzar da zaman lafiya da daidaito acikin al’umma.
Kwamitin na ƙarƙashin jagorancin Alhaji Lawal Rufa’i Safana, mai mai wa gwamna shawara kan sashen kula da lamurran ƙananan hukumomi.
Barista Faskari, ya bayyana wannan rikici a matsayin abin takaici, inda ya umarci kwamitin da ya gudanar da sahihin bincike domin gano ainihin adadin ɓarnar da aka yi da ɗaukar matakan kare afkuwar irin haka a nan gaba.
A jawabin sa shugaban Kwamitin Alh. Lawal Rufa’i Safana ya bayyana ƙudurin su na ganin sun safke nauyin da aka ɗora masu bisa gaskiya da adalci.
Kwanan baya ne rikici ya ɓarke a tsakanin al’ummomin ƙauyen Rijiyar Tsamiya a ƙaramar hukumar Sandamu da ƙauyen Minawa da ke ƙaramar hukumar Dutsi inda aka rasa rayuka da asarar dukiya.
