’Yan Nijeriya miliyan 31 na fama da ƙarancin abinci — MDD

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar kula da ayyukan jinƙai ta Majalisar ɗinkin Duniya, ta nuna damuwa kan yadda matsalar yunwa da talauci da kuma rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Nijeriya.

Hukumar ta ƙiyasta cewa sama da mutane miliyan 31 na fama da ƙarancin abinci a faɗin Nijeriya.

Hukumar ta ƙara da cewa akwai yara ƙanana sama da miliyan 10 ’yan ƙasa da shekara biyar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Wannan bayani ya fito ne a wani taro da Gwamnatin Tarayya tare da hukumar suka shirya a Abuja, domin bikin Ranar Jinƙai ta Duniya ta shekarar 2025.

Taken bikin na bana shi ne: “ƙarfafa haɗin gwiwa da taimaka wa al’umma.”

Jami’in hukumar jinƙai na Majalisar ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohamed Fall, ya ce ana fuskantar babban ƙalubale sakamakon ƙaruwar buƙatar tallafi a ƙasar.

Ya nuna damuwa kan yadda taimakon jinƙai daga ƙasashe ke raguwa.

Ya jaddada cewa akwai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin rage barazanar yunwa da matsalar rashin abinci mai gina jiki a Nijeriya.

By ukarofi