Saudiyya ta ƙaddamar da sabon tsarin Umrah don sauƙaƙe ziyara

Spread the love

A ranar 20 ga Agusta 2025, gwamnatin Saudi Arabia, ta hannun Ma’aikatar Hajj da Umrah, ta ƙaddamar da wani sabon tsarin zamani mai suna “Nusuk Umrah”, wanda ya shafi dukkan musulmi da ke son gudanar da ziyarar Umrah daga ko ina a duniya.

Sabon tsarin yana bai wa masu niyyar zuwa Umrah damar yin rajista da neman visa ta yanar gizo kai tsaye, tare da haɗa shi da sauran sabis na balaguro da masauki a Makkah da Madina a wuri guda. Wannan yana nufin cewa, ba sai mutum ya riƙa bi ofis-ofis daban-daban ba, dukkan ayyukan za a yi su cikin sauƙi, sauri, da tsari na zamani.

Manufar wannan sabon tsarin na daga cikin Vision 2030, shirin gwamnatin Saudi Arabia na sabunta tattalin arzikinta da rage dogaro da man fetur, tare da ƙara samar da damammaki ta fuskar yawon shaƙatawa da ziyara.

Haka kuma, gwamnatin ta ce, sabon tsarin zai taimaka wajen ƙara yawan baƙin da ke zuwa ƙasar daga ƙasashe daban-daban, musamman daga yankin Asiya da Afirka, inda miliyoyin musulmi ke da sha’awar yin Umrah duk shekara.

Masu sharhi sun bayyana cewa, wannan sabon mataki zai zama babban sauyi ga harkar addini da turizim a Saudi Arabia, musamman ganin cewa yanzu alhazai za su iya tsara duk tafiyarsu daga gida har zuwa lokacin dawowa ba tare da wahala ba.

By ukarofi