Sakatare-Janar na Majalisar ɗinkin Duniya (MDD), António Guterres, ya fitar da sanarwa a jiya Alhamis 21 ga Agusta 2025 inda ya yi kira da a dakatar da dukkan hare-hare a Gaza nan take, musamman bayan da hukumomin Isra’ila suka bayyana aniyarsu ta ƙaddamar da sabon babban farmaki a Gaza City.
Guterres ya bayyana cewa, duk wani sabon farmaki a wannan lokaci zai zama mummunar barazana ga rayukan fararen hula, musamman la’akari da cewa Gaza ta riga ta kasance cikin halin ƙunci da yunwa bayan watanni na tashin hankali da kullen da Isra’ila ta yi.
Sakatare-janar ɗin ya kuma yi kira da a saki ba tare da sharaɗi ba duk fursunonin da ake riƙe da su, musamman mata da yara, ya na mai jaddada cewa ci gaba da tsare waɗannan mutane ba kawai cin zarafi ba ne, har ma ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Haka kuma, ya nuna damuwarsa game da matakin Isra’ila na ƙara gina sabbin matsugunnai a West Bank, wanda ya ce zai iya rushe duk wata dama ta mafarkin ƙasa biyu, wato Isra’ila da Falasdinu wanda duniya ta daɗe tana aiki a kai.
Wannan kiran na zuwa ne a lokacin da ake ƙara samun rikici a siyasar duniya dangane da rikicin Gabas ta Tsakiya, inda ƙasashe kamar Jordan, Faransa, Jamus, da Birtaniya suka bayyana adawa da sabon tsarin na Isra’ila, yayin da wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya suka yi kira da a kawo ƙarshen jinin da ke zuba a Gaza.
