Badaƙala: EFCC na neman sirikin Atiku, Bashir Haske ruwa a jallo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ayyana sirikin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar kuma ɗan kasuwa, wato Abdullahi Bashir Haske a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa zargin sa da hannun a badaƙalar wasu kuɗaɗe.

Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya bayyana hakan a wata takarda da aka sanya a allon sanarwar ofishinsu, ranar Alhamis.

A cewar EFCC, Haske mai shekaru 38 yana da hannu a kitsa makircin babban laifi da kuma sauya akalar wasu kuɗaɗe.

Don haka hukumar ta wallafa hotonsa a takardar da sunan tana nemansa ruwa-a-jallo.

Ta ce, ganin sa na ƙarshe shi ne wanda aka yi a No. 6 hanyar Mosley da ke yankin Ikoyi da layin Idejo da ke Victoria Island a jihar Legas.

Akan haka ta yi kira ga ƴan Nijeriya du su taimaka mata da rahoton zirga-zirgarsa ta hanyar sanar da kowane ɗaya daga cikin ofisoshinta a ƙasar.

Daga cikin su akwai na Abuja, Lagas, Fatakwal, Kano, Ibadan, Enugu, Ilorin, Kaduna, Sakkwato, Maiduguri, Benin, Makurɗi, Uyo, da kuma Gombe.

By Babaji