
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya kirayi al’ummar Nijeriya da su koyi yadda za su riƙa kare kansu daga farmakin miyagu saboda ko ta-kwana.
Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Janar Musa ya ce horon kare kai abu ne mai muhimmanci ga ɗan Nijeriya kamar yadda koyon tuƙi ko ninƙaya acikin al’umma ke da muhimmanci a hali na yaƙi ko akasin haka.
“A Turai, ninƙaya wajibi ne. Koyo da karantarwa akan tsaro ma wajibi ne, saboda sai ka san mene ne tsaro.”
Haka kuma, Babban Hafsan ya ce akwai buƙatar a sabunta tsarin gudanar da aikin hidimar ƙasa ta NYSC ta yadda za a riƙa koyar da masu yi salon kare kai ba tare da makami ba.
Janar Musa ya jaddada muhimmanci koyar da matasa kare kansu daga miyagu da ke ƙoƙarin cutar da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
Kazalika, ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su kasance masu kula da sanya ido akan ababen da ke faruwa a yankunansu, yana mai cewa tsaro ba alhakin gwamnati ba ne kaɗai, saidai abu ne da ya shafi kowane ɗan ƙasa.
