Alƙalin ‘Viral TV’, Frank Caprio ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Frank Caprio, wanda daɗaɗɗen Alƙali ne na kotun birni ta ‘Providence Municipal’ a Amurka kuma shahararre a kafar talabijin, ya rasu bayan shafe shekaru 88 a duniya.

Ɗansa, Frank T. Caprio ya sanar da hakan a ranar Laraba a wani rubutu ta Facebook a madadin iyalan marigayin.

Ya ce, mahaifin nasu “ya rasu ne cikin aminci yana da shekaru 88 bayan fama da cutar daji ta ƙundu ta tsawon lokaci.”

Marigayin sananne ne akan tsayar da gaskiya da adalci a matsayinsa na alaƙali da ma wajen haka, lamarin da ya sa ya zama jigo kuma abin kwaikwayo acikin al’umma.

Ya kuma ce, za a cigaba da tunawa da shi a matsayin alƙali kuma uba na gari, wanda ya sadaukar da kansa ga iyalansa da ɗaukacin al’umma.

A shekarar 1985 Caprio ya zama Alƙalin Kotun Municipal inda ya yi aiki har na tsawon kusan shekaru arba’in a muƙamin.

Baya ga haka, ya samu kyautuka da dama a mataki na ƙasa da ƙasa-da-ƙasa duba da yadda ya ke yin hukunci akan lamuran da suka shafi taka dokar gudanar da tituna ga masu ababen hawa cikin gaskiya da adalci.

Haka ma a fannin shirye-shiryen gidajen talabijin akan aikinsa na alƙalanci, inda ya riƙa haskawa har na tsawon shekaru ashirin.

By Babaji