
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya kirayi al’ummar Nijeriya da su jarraba sabon na’urar lissafa haraji da gwamnatinsa ta ƙaddamar, domin ƙididdige abinda za su riƙa biya a ƙarƙashin sabon tsarin haraji da aka sanya a doka.
A wani rubutu ta shafin X ranar Alhamis, Tinubu ya ce na’urar za ta taimaka wa ɗaiɗaikun mutane lissafa adadin kuɗaɗen harajin da ke kansu a sabon tsarin, wanda za a fara aiwatarwa a shekara mai kamawa.
Ya kuma ce, tsarin haraji na ‘fair tax’ ba abu ne da zai magance talauci ba ko ƙara nauyi akan marasa galihu, saidai zai taimaka wajen sauƙaƙe fahimtar hanyoyin biya.
Shugaban ƙasar ya bayyana cewa, an gabatar da sabon tsarin harajin ne da nufin samar da daidaito da tabbatar da gaskiya da adalci akan harkar tattalin ƙasa.
Lamarin da acewarsa sabunta fata ne ga al’umma a Nijeriya.
Za a iya samun na’urar lissafin ta adireshin yanar gizo kamar haka: https://fiscalreforms.ng/index.php/pit-calculator.
