Ali Nuhu ya rattaɓa hannu don cimma tsare-tsaren Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tawagar Hukumar Kula da Fina-finan Nijeriya NFC, ƙarƙashin jagorancin Darakta Manajanta, Ali Nuhu, ta halarci taron masu ruwa da tsaki don raya al’adu a Ma’aikatar Al’adu da Ƙirƙira.

An gudanar da zaman, wanda aka yi wa take da ‘Strategic Repositioning of Nigeria’s Art, Culture, Tourism and Economy for National Development and Competitiveness’ a ƙarƙashin jagorancin Ministar Ma’aikatar, Barista Hannatu Musawa.

Haka kuma, an shirya taron ne na kwana biyu da nufin haɗe dabarun ma’aikatar da manufofin ci-gaban gwamnati wajen faɗaɗa alaƙar hukumomi da samar da ci-gaban ayyuka da tsare-tsaren aiwatarwa.

Babban abinda aka cimma a zaman shi ne sanya hannu akan yarjejeniyar tafiyar da ayyukan ma’aikatar a tsakanin minitsar, babban sakatare, shugabanni da daraktocin hukumomi gami da ƙoƙarin aiwatar da tsare-tsaren ma’aikatar yadda suka dace.

A wata takarda daga NFC, hukumar ta ce tana aiki tuƙuru wajen taimaka wa ayyuka da shirye-shiryen ci-gaba na gwamnati musamman wajen samar da yanayi mai kyau a gare su.

Kazalika, tana ƙoƙarin bada horo da damanmaki wajen inganta ayyukan ci-gaba a ƙasa don amfanin gwamnati da al’umma baki ɗaya.

By Babaji