Ba na yunwar zama shugaban ƙasa, inji Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya ce burinsa shi ne Nijeriya ta gyaru, ba manufar kai ta zama shugaba ba.

Da yake magana a taron karɓar wasu sababbin mambobin jam’iyyar ADC ranar Asabar a Legas, Atiku, wanda ya samu wakilcin Farfesa Ola Olateju na Jami’ar Achievers da ke Owo, ya ce tafiyar siyasarsa ta ginu ne akan shugabanci na gari da ci-gaban ƙasa.

“Shirin Atiku Abubakar shine a gina ingantacciyar ƙasa. Ba wai akan shi a karan kansa ya zama shugaba ko ta wace hanya ba. Abinda aka damu da shi shine a samu gwamnati da za ta yi wa al’umma hidimar da ta dace”, inji Olateju a madadinsa.

Atiku, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa ADC tare da wasu jiga-jigan ƴan ɓangaren adawa, ya bayyana jamiyyar a matsayin tafiyar da za ta samar da shugabanci na gari a Nijeriya.

Ya ce, ADC ta shiyar wajen ganin ta yi duk abinda ya dace wajen magance matsalolin da suka addabi al’umma a ƙasar musamman akan matsin rayuwa tun daga cire tallafin fetur.

Kazalika, game da wanda zai tsaya takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar, ya bayyana cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci, sannan a bai wa wanda ya yi nasara.

By Babaji